Tukur Mamu ya karɓi miliyan N50 daga kuɗin fansar harin jirgin ƙasan Kaduna – DSS

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar tsaro ta DSS ta zargi ɗan jarida kuma mai shiga tsakani da ’yan ta’addar da suka sace fasinjojin jrigin ƙasan Kaduna-Abuja a shekarar 2022, Tukur Mamu, da karɓar Naira miliyan 50 daga kuɗin fansar fasinjojin.

Mamu na fuskantar tuhumar laifukan ta’addanci, ciki har da karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin Kaduna na ranar 28 ga Maris, 2022, hulɗa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, hana aikin kwamitin babban hafsan tsaron ƙasa da aka kafa domin tattaunawa da masu garkuwa da mutanen, musayar saƙonnin murya da mai magana da yawun Boko Haram, da sauransu.

A ci gaba da shari’ar a ranar Talata, shaida na hukumar ta DSS na shida ya shaida wa kotu cewa ƙungiyar ta’addan ta nemi Mamu ya koya musu yadda ake buɗe shafin yanar gizo domin gudanar da ayyukansu.

Tun da farko, DSS ta bayyana cewa Mamu ya ba da shawara ga ƙungiyar ’yan ta’addan da su tattauna kai tsaye da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su, ba tare da shiga kwamitin babban hafsan tsaron da gwamnatin tarayya ta kafa ba.

Shaidar ya yi wannan bayani ne yayin fassara saƙonnin murya na Mamu a lokacin da ake yi masa tambayoyi a ƙasar Masar kafin a dawo da shi Nijeriya.

A halin yanzu, Mamu ya shigar da Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa kiran shi da dan ta’adda.

Ya ce ya shigar da ƙarar ce kan kiran nasa da dan ta’adda da ministan ya yi, alhali ana tsaka da shari’ar tuhumar laifukan ta’addanci kuma har yanzu ba a kai ga yanke hukunci ba.

Alƙali ya dage shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun 2026, domin amincewa da jawaban ƙarshe na ɓangarorin da abin ya shafa bisa tanadin Sashe na 49 na Dokar da kuma Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

By ukarofi