
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), ta gayyaci tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, (SAN).
A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, Malami ya ce hukumar ta gayyace shi ne domin ya yi bayani akan wasu abubuwa da bai bayyana ba inda ya bada tabbacin girmama gayyatar.
“A matsayina na ɗan ƙasa mai bin doka da oda kuma mai kishin ƙasa, na kuduri aniyar girmama wannan gayyata. Na yi imani da muhimmancin gaskiya, riƙon amana da kuma rike gaskiya a harkokin mulki — waɗannan ƙa’idoji ne da na dade ina goyon baya tare da tsayawa a kai, a iya shekaru danayi a aikina na hidimar jama’a” kamar yadda ya wallafa a shafinsa.
Tsohon ministan ya kuma shaida wa ƴan ƙasar zai ci gaba da sanar da su abin da zai biyo baya, a cewar sa ‘domin kowa ya kasance da masaniyar me zai je ya koma saboda halin rayuwa na yau da gobe da kuma tarihi.”
