
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cikakken goyon bayansa ga dokar ta-ɓaci akan lamuran tsaro da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a ƴan kwanakin bisa la’akari da ƙamarin taɓarɓarewar harkokin tsaro a sassan Nijeriya.
Ya ce, lokaci ya yi da za a ƙara matsa ƙaimi wajen murƙushe ƴan fashi da masu garkuwa da mutane.
Ya bayyana cewa Kano za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare al’umma, musamman yankunan iyaka da suka fuskanci hare-hare kwanan nan, inda aka sace mutane tare da tayar da hankulan jama’a.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta yi shiru ba, kuma za ta tashi tsaye wajen kawar da barazanar ta’addanci a jihar.
Haka kuma, ya koka game da matsalolin tsaro da suka fara addabar al’umma a wasu yankunan jihar, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da bada kariya ga rayuka da dukiyoyi.
Kazalika, ya yaba wa al’ummar jihar bisa cigaba da ba gwamnatinsa goyon baya da amanna da tsare-tsaren wajen jagoranci.
