
A yammacin jiya Alhamis ne tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya koma Abuja bayan an ɗauko shi daga Guinea-Bissau sakamakon karɓe mulkin ƙasar da sojoji suka yi, inda ya sauka a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayya Abuja.
Hotunan faifan bidiyo na isowarsa, wanda kafar yada labarai ta ARISE ta yada, ya nuna Jonathan yana saukowa daga matakalar jirgin gwamnatin Guinea-Bissau cikin dare, inda ya samu tarba daga dimbin magoya baya da jami’ai.
Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban tawagar dattawan Afrika ta Yamma don sa ido kan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.
Har yanzu tawagarsa na cigaba da gudanar da aikinta a lokacin da sojoji suka sanar da cewa sun karbe ikon gwamnati.
Biyo bayan rahotannin da ke cewa Jonathan ya makale, Majalisar Wakilai a zamanta na ranar Alhamis ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta tura duk wata kafar diflomasiyya domin ganin tsohon Shugaban ya dawo lafiya.
Daga baya gwamnatin tarayya ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da cewa Jonathan na cikin koshin lafiya kuma ya bar kasar Guinea-Bissau.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan yana cikin koshin lafiya kuma ya fita daga kasar Guinea-Bissau. Ya tafi da jirgin sama na musamman tare da ‘yan tawagarsa, ciki har da Mohamed Chambas,” inji kakakin ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, a wata hira da manema labarai.
Kasar Guinea-Bissau ta fada cikin rudani ranar Laraba bayan da jami’an soji suka bayyana cewa sun karbe ikon kasar baki daya, sun rufe iyakokinta, da kuma dakatar da ayyukan zabe.
An bayar da rahoton cewa, an yi ta harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasar, yayin da sojoji suka yi shingen muhimman hanyoyin shiga babban birnin kasar.
