Lamiɗo ya nemi a kafa kwamitin riƙo don tafiyar da harkokin PDP

Spread the love

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Sule Lamido, ya bayar da wa’adin kwanaki goma ga jam’iyyar na ta magance magance rikicin cikin gida da ya dabaibaye ta kuma yake ƙoƙarin dagula al’amuran siyasarta.

Ya kuma yi kira da a rusa zaɓen Ibadan da aka yi a babban taron jam’iyyar na kwanan nan tare da kafa kwamitin riƙo na ƙasa a nan take.

Lamiɗo ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga magoya bayansa ciki har da tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi, tsoffin kwamishinoni, da sauran ƴan siyasa, wadanda suka kai masa ziyarar goyon baya a ofishinsa na Sharada da ke jihar Kano.

Tsohon gwamnan ya nuna damuwa game da rikicin da ke cikin jam’iyyar, yana mai cewa masu ruwa da tsaki da suka daɗe kamar shi sun rasa goyon bayan sabbin masu faɗa-a-ji na cikin jam’iyyar.

“Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar a yanzu yana da alaƙa da ƙoƙarin da ake yi na rage muhimmancin siyasata”, inji shi.

Ya yi gargaɗin cewa matuƙar aka rasa tsarin jagoranci mai kyau acikin PDP, to hakan zai zama barazana ga masu riƙe da muƙamanta da masu neman a sake zaɓar su.

Don haka ya yi kira ga jagororinta da su kira taron haɗaka domin warware dukkan ƙalubalen da jam’iyyar take fuskanta tare da dawo da martabarta a siyasance.

By Babaji