A rage ayyukan Majalisar Dokoki don ƙarfafa tsaro – Ndume ga Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya nemi a rage wasu ayyukan gwamnati ciki har da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin wata hanya ta rage adadin kuɗaɗen da gwamnati take kashewa domin ƙarfafa ayyana fannin daƙile ta’addanci ta fuskar kuɗi a Nijeriya.

A wata hira da Channels Television da ya yi ranar Alhamis, Ndume ya ce nauyin kuɗin gudanar da Majalisar Dattawa a tsarin cikakken lokaci ba zai ɗore ba, musamman a wannan lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin kuɗi da tsaro.

Ya ce, “kudin gudanar da gwamnati ya yi yawa. Idan ‘yan majalisa za su yi aiki na wucin gadi, gwamnati za ta ajiye biliyoyin naira,” inda ya nuna cewa za a iya mayar da waɗannan kuɗaɗen zuwa ga tsaro, diflomasiyya da wasu muhimman abubuwan ƙasa.

Ndume ya alaƙanta tsadar gudanar da gwamnati da matsalolin da ke hana ƙasar yaƙi da rashin tsaro yadda ya kamata.

Ya ce, Nijeriya ba za ta iya kashe kuɗaɗe marasa amfani ba a lokacin da take fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, garkuwa da mutane a Arewa Maso Yamma da Arewa-Tsakiya da kuma satar mutane da tashin hankali.

A matsayin wani bangare na gwagwarmayar rage kashe kuɗi, sanatan ya soki kasancewar ‘yan sanda da yawa suna kewaye ‘yan majalisa da wasu manyan jami’an gwamnati duk da umarnin Shugaba Bola Tinubu na janye masu tsaron manyan mutane.

Shugaban ya kuma umarci IGP Kayode Egbetokun ya mayar da ‘yan sanda daga tsaron VIP zuwa ayyukan tsaro na gaba.

Sanata Ndume ya ce tsarin tsaro na ƙasa yana fuskantar matsin lamba kuma yana buƙatar “duk wani jami’in da ake da shi,” yana mai jaddada cewa dubban jami’an suna rataye ga ‘yan siyasa da masu tasiri waɗanda za su iya yin aiki ba tare da irin wannan tsaro mai nauyi ba.

Ya yi kira ga Shugaba Tinubu da hukumomin ‘yan sanda da su gaggauta aiwatar da sauye-sauyen da ake yi, inda ya jaddada cewa jami’an dole ne su mayar da hankali wajen kare jama’a baki ɗaya maimakon ɗaiɗaikun mutane.

By Babaji