Mikel Obi na harin aikin shugabancin NFF

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Bayan da Super Eagles ta gaza nasarar shiga gasar Kofin Duniya na 2026 karo biyu a jere, tsohon wasan tsakiya ma Nijeriya da ƙungiyar Chelsea, John Obi Mikel ya bayyana aniyarsa ta karɓar jagorancin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta ƙasa (NFF).

Tsohon kyaftin ɗin na Super Eagles ya ce shigarsa harkokin ƙwallon Nijeriyar za ta taimaka wajen tabbatar da gaskiya da adalci tare da kauce wa dukkan ayyukan da suka shafi rashawa a hukumar.

Ya bayyana cewa, wajibi ne a sanya koma a gurbinsa tare da yaƙar duk wata hanya da za ra bada damar rashawa.

Mikel, wanda tsohon tauraron ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ne, ya jima yana sukar tsarin gudanarwar NFF.

A baya ya yi kira ga baki ɗaya jami’an hukumar gudanarwar NFF da sauka daga shugabanci hukumar bisa abin da ya kira da ‘rashin tsare aiki da rashawa’, wanda a cewarsa, sune dalilan lalacewar Super Eagles.

By Babaji