Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Wani shahararren marubuci daga Kano, Kabiru Ahmad Kwalli, ya kammala rubuta sabon littafinsa mai taken “Mu San Magabata”, wanda ya tattara tarihin fitattun mutanen Kano 24 da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jihar a fannoni daban-daban.
Yayin taron manema labarai a Mustibrah Polytechnic, Kano ranar Alhamis, Kwalli ya ce manufarsa ita ce cike gibi wajen rubuce rubucen tarihi, ganin cewa yawancin manyan mutanen Kano ba su da cikakkun kundin tarihin rayuwarsu, duk da gagarumar gudummawar da suka bayar.
Littafin ya yi duba ne kan shugabanni, malamai, ’yan kasuwa da jajirtattun masu hidimar al’umma da suka yi fice a tarihi. Fitattun sunayen da aka ambata sun haɗa da:
Madakin Kano Shehu Ahmad, Alƙalin Kano Umaru, Sheikh Sani Auwalu Darma, Alhaji Uba Ringim, Alhaji Imam Wali, Alhaji Ado Dandolo,
Malam Nura Alƙali, Malam Adamu Aminu.
Sauran sun haɗa da: Kansila Malam Ahmadu Rufa’i Daura, Alhaji Barau Maiwake, Alhaji Baballe Ila, Alhaji Baffa Yola, Alhaji Muhammadu Yankwashi Kazaure, Alhaji Mahe Bashir Wali, Alhaji Salisu Sambajo da Alƙali Husaini Sufi da dai sauran sanannun jaruman al’umma har zuwa mutum 24.
Kwalli ya bayyana cewa wannan littafi shi ne juzu’i na farko, domin yana da nufin ci gaba da rubuta tarihin malaman addini, shugabannin gargajiya, ’yan kasuwa, matan jarumai da sauran manyan mutane da suka inganta Kano da ƙasa baki ɗaya.
Kazalika, an kafa Kwamitin Kaddamarwa ƙarƙashin jagorancin Farfesa Bashir Yusuf, tare da Alhaji Ibrahim Aminu Dan’lya da Alhaji Ali Adamu a matsayin mataimaka, sannan Abubakar Farouk Kabara a matsayin sakatare.
Daga nan marubucin ya gode wa dukkan waɗanda suka mara masa baya, tare da kira ga al’umma da su inganta al’adar rubuta tarihi domin adana gadon magabata da kuma ƙarfafa fahimtar al’umma.
