‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Bakori ya sanar da haka a wata hira da manema labarai,ya bayyana cewa cikin waɗanda a ka sako mutane 17 mata ta ne ,18 kuma maza sai yara ƙanana guda biyu.
Ya ce ‘ywn bindigan su sako mutanen sakamakon sasanci da al’ummar yankin sukayi da ƴan bindigan kuma ko kobo a bayar ba.
Kandarawa ya yi godiya ga Allah da yanayin da ya ga mutanen da suka shafi iskar yanci cikin ƙoshin lafiya.
Ya ce ya zuwa yanzu babu Mutum ko ɗaya da ke hannun yan bindigan, ɗan majalisar ya ce.
Ɗan majalisar dokokin sai yayi kira da al’ummar yankin da cigaba da zaman lafiya a tsakaninsu.
A ɓangaren yan bindigan ƙarƙashin jagorancin ƙasurgumin ɗan bindiga Isiya kwashen Garwa ya jagoranci Sakin mutanen.
