MOPPAN ta jajenta rasuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa MOPPAN, ta yi alhinin rashin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis.

A wata takarda daga Shugabanta, Shehu Hassan Kano, MOPPAN ta ce a madadin mambobinta, tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalai, ƴan uwa, ɗalibansa da ɗaukacin al’ummar Musulmi bisa rashin marigayin.

MOPPAN ta bayyana cewa, rashin shehin malamin ya haifar da babban giɓi ga al’ummar musulmi musamman ƴan Ɗarikar Tijjaniya duba da hidimarsa ta koyar da addinin Musulunci da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya acikin al’umma.

Ƙungiyar ta kuma ce, za a cigaba da tuna marigayin bisa karantarwarsa musamman fannin tafsiri da karatun Alƙur’ani mai girma gami da kyawawan ayyukansa a matsayinsa na jagora.

A ƙarshe, ta yi masa addu’ar Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa da fatan shiga Aljannar Firdausi, gami da ba makusantansa haƙurin juriyan rashin sa.

By Babaji