
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta sallami tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami sa’o’i kaɗan bayan amsa gayyatar ta yi masa.
Malami (SAN), ya bayyana haka ta kafar Facebook inda ya ce, EFCC ta sallame shi, bayan ya amsa wasu tambayoyi da take neman amsarsu daga gare shi.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jim kaɗan bayan fitowa daga ofishin hukumar, Malami ya ce, yana gode wa Allah da ya ba shi ikon kammala amsa tambayoyin hukumar lafiya.
Ya kuma ce, ganawar tasa da jami’an EFCC ta kasance mai kyau domin an gudanar da ita busa tsari ba tare da wsni yunƙuri na ba shari’a wahala ba.
Saidai ya ce, hukumar ta sake sanya wani lokaci, domin ya sake halarta ofishinta domin cigaba da ganawar.
Malami shi ya riƙe muƙamin Ministan Shari’a kima Antoni Janar na Ƙasa a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023.
