Za a rataye ɗalibin Jami’ar UNIPORT kan halaka budurwarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Jihar Ribas da ke zaune a Fatakwal, ta yanke wa wani ɗan ajin ƙarshe na Jami’ar jihar (UNIPORT) mai suna Damian Okoligwe, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifin halaka budurwarsa, Justina Otuene.

An samu Okoligwe ne da laifin kisan Otuene a ranar 20 ga watan Oktoban 2023 a gidansa da ke Mgbuoba a Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor da ke jihar.

Bayan haka ne sai kuma ya daddatsa gangar jikinta, sannan ya zuba ta a baro da nufin zubarwa a matsayin shara, inda a yayin haka ne aka cafke shi.

Al’amarin, ya haddasa firgici da cecekuce acikin al’umma, wanda hatta lauyoyin da suka tsaya akan ƙarar sun bayyana hakan a matsayin abin takaici.

Da yake gabatar da hukunci a ranar Juma’a, Mai Shari’a Chinwe Nsrim-Nwosu ya tabbatar da cewa hujjojin da aka gabatar akan mai laifin sun gamsar da kotun akan shi ya aikata.

Don haka ya bayar da umarnin a rataye shi har sai ya mutu a matsayin sakamakonsa.

A nasa jawabin, lauyan ɓangaren da ya shigar da ƙara ya ce ya gamsu da hukuncin, yana mai bayyana hakan a matsayin darasi ga ƴan baya ko masu shirin aikata irin laifin.

By Babaji