Haihata-haihata ni da makaranta – Ɗalibin da ya kuɓuta bayan garkuwa da ƴan makarantar Neja ya faɗi halin da ya tsinci kansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani ɗalibi mai suna Stephen Samuel mai shekaru 13, wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a makarantar St Mary’s Catholic School, Papiri ta Karamar Hukumar Agwaran Jihar Neja, ya bayyana halin da ya tsinci kansa a ciki bayan ya samu tsira, inda ya ce yana ganin shi da makaranta har abada.

Da yake magana yayin hira da jaridar Reuters, Samuel ya bayyana cewa ƴan bindigar sun far musu da tsakar dare a lokacin da suke barci, inda suka tashe su tare da umartar su da su kwanta.

A lokacin ne suka ɗaure musu hannaye tare da tilasta musu tsayuwa kana daga bisani suka tasa ƙeyarsu zuwa jeji.

Yaron ya ƙara da cewa, ya samu kuɓuta ne a lokacin da babur ɗin ɗaya daga cikin ƴan bindigar ya lalace: “Na gudu. Bai ganni ba. Ban ma san inda za ni ba – ni dai na cigaba da gudu”, inji shi.

Ana tsaka da haka ne sai ya tsinci kansa a wata gona inda ya haɗu da wani maƙocinsu, wanda ya ba shi kayan sawa, sannan ya koma gida cikin salama.

A ranar 21 ga watan Nuwamba ne ƴan bindiga suak farmaki makarantar, inda suka yi awon-gaba mutane 315 da suka ɗalibai 303 da malamai 12.

By Babaji