ECOWAS ta dakatar da Guinea-Bissau kan juyin mulki

Spread the love

Ƙungiyar Tattalin Arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, ta dakatar da ƙasar Guinea-Bissau daga dukkan fannonin aiwatar da shawararta bayan juyin mulkin da ya hambarar da Shugaba Umaro Sissoco Embaló.

Sanarwar ta fito ne bayan taron gaggawa da shugabannin ƙasashen suka gudanar, inda suka yi Allah-wadai da juyin mulkin tare da bukatar a mayar da mulki kan tsarin dimokuraɗiyya ba tare da wani sharadi ba.

Kungiyar ta yi kira da a saki Shugaba Embaló da sauran jami’an zaɓe da ke tsare, sannan ta dage cewa dole ne a ba Hukumar Zaɓe damar bayyana sakamakon zaɓen 23 ga Nuwamba ba tare da jinkiri ba.

ECOWAS ta gargadi waɗanda suka jagoranci juyin mulkin cewa za a ɗauki mataki a kansu, tare da umartar samar da kariya ga masu sa ido na ƙungiyar da na ƙasashen duniya.

Shugabannin ƙasashen yanki, manyan jami’an ECOWAS, Tarayyar Afirka, da majalisar dinkin Duniya sun halarci taron gaggawar da aka gudanar ta yanar gizo.

By Babaji