Ƙungiyar AU ta dakatar da Guinea-Bissau kan juyin mulki

Spread the love

Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), ta dakatar da ƙasar Guinea-Bissau daga zama memba, sakamakon kifar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissico-Embalo da dakarun sojoji suka yi a makon da ya gabata.

Shugaban ƙungiyar, Mahamoud Youssouf, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Juma’a.

Wannan matakin na AU ya biyo bayan ƙararrawar da ECOWAS ta ɗauka a sa’o’i kafin haka, inda ita ma ta sanar da dakatar da Guinea-Bissau daga yalwar ayyukanta, bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar.

An gudanar da juyin mulkin ne yayin da ake cigaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, wanda manyan ƴan takarar kujerar biyu suek ikirarin nasara.

By Babaji