Basaraken Zamfara ya yi kira ga iyaye da su sanya ‘ya’yansu makaranta

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sarkin Ƙaura Namoda a Jihar Zamfara, Alhaji Sanusi Ahmed Muhammad Asha ya buƙaci iyaye da su fifita ilimin ‘ya’yansu don samun kyakkyawar makoma musamman wajen tabbatar da sanya su a makarantun boko da na Islamiyya.

Sarkin ya bayar da shawarar ne yayin da yake jagorantar bikin yaye ɗalibai 432 na kwalejin Ahmad Asha ta Nazarin Larabci da Musulunci dake a garin Ƙaura Namoda, da aka gudanar a Kwalejin Fasaha da Kerekere ta tarayya da ke Ƙaura Namoda.

A cewarsa, ilimi ginshiƙi ne na gina al’umma, don haka akwai buƙatar iyaye, masu kula da yara da duk masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa wa ‘ya’yansu gwiwa su sami damar shiga ilimin boko dana musulunci a masarautarsa.

“Na yi imanin cewa ilimi shine mafi muhimmanci ga yara don samun ingantacciyar zuriya mai zuwa”. Sarkin ya ce

Sarkin ya ƙara da cewa masarautarsa ta ƙuduri aniyar tallafawa yara masu rauni don samun damar samun ilimin boko da ilimin addinin musulunci.

“Muna tabbatar da cewa kowane yaro ya sami damar samun ilimin boko da na musulunci ta hanyar haɗin gwiwa da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki don samun ingantattun alumma a masarautar mu.” Alhaji Sanusi Muhammad Asha ya ce

Ya kuma taya mahardata 432 na Alƙur’ani waɗanda suka yi nasarar kammala karatunsu a cibiyar nazarin larabci da musulunci ta Ahmad Asha a Masarautar shi.

Ya roƙe su da su ilmantar da wasu ilimin da suka samu don samun ingantacciyar al’umma a masarautar.

Basaraken ya yaba wa sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, saboda goyon bayansa ga cibiyar nazarin larabci da musulunci ta Ahmad Asha, yana mai kira ga masu hannu da shuni a masarautar da su yi koyi da shi don ci gaban cibiyar.

By ukarofi