Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An ƙaddamar da littafin tarihin Gwamnan mulkin soja na farko na jihar Kano, Alhaji Audu Baƙo mai suna “Governor Audu Bako Man of Wisdom and Foresight, wanda Kwamishinan ‘yan sanda mai ritaya Dogo Manya ya rubuta.
Taron an gudanar da shi ne a Kano da ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na jihar Kano da Jigawa wato tsohuwar jihar Kano da suka haɗa da mataimakin Gwamnan jihar Jigawa Ahmad Usman Gumel da Kwamishinan ma’aikatar kasuwanci na jihar Kano Gwani Wada Sagagi wanda ya wakilci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a yayin taron.
Babban mai ƙaddamar da littafin Alhaji A.A. Rano wanda ya samu wakilcin ɗan uwansa Alhaji Wada A A Rano ya ƙaddamar da sayen littafin guda 25 akan N25,000,000 shi kuma ya sayi kwafi 10 akan N500,000 jama’a da dama ne dai suka ƙaddamar da sayen littafin.
Ambasada Hajiya Zainab Audu Baƙo ɗaya daga cikin ‘ya’yan Marigayi Alhaji Audu Baƙo tsohon Gwamnan jihar Kano na farko ta shaidawa ‘yan jarida mutuƙar jin daɗi da farin cikinsu bisa rubuta littafin da ya ƙunshi irin halayyar mahaifnsu da suka yi aiki tare tsawon lokaci.
Ta yi nuni da cewa ana ganin irin ayyuka da ya yi ana cewa Audu Bako ne ya yi amma mutane basu fahimci wanene shi ba ganin shi marubucin littafin yana tare dashi ya sanshi da irin tunanin shi, akwai abinda ya sani game dashi da al’umma basu sani ba shine ya wallafa littafin.
Ya ce duba da yanda yanzu shugabanci ke tafiya a ƙasar nan babu kishi,babu damuwa da tausayin talaka, ba gaskiya da amana saɓanin a lokacin mahaifinsu sun yi aiki tuƙuru ba tare da taɓa haƙƙin al’umma ba, don haka suna godiya ga Allah gaskiyar mahaifinsu ya daɗa bayyana, littafin zai zama izina ga masu mulki da matasa masu tasowa su karanta su fahimci yanda yayi kyakkyawan shugabanci domin a gyara lamarin.
Ambasada Hajiya Zainab Audu Baƙo tace suna jin daɗin idan ana faɗar ayyukan alheri da mahaifinsu yayi da alfahari dashi suna roƙon Allah yasa subi sawunsa wajen aikata ayyuka nagari ya tsare su da duk wani abu na ba daidai ba sun godewa Allah da mahaifinsu da mahaifiyarsu suka bar musu baya mai kyau wanda har gobe ana faɗar magana mai daɗi akansu sun kafa tarihin abinda ke amfanar da al’umma .
Ta yi kira ga Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf akan ta taimaka ta ƙarasa mallaka sauran kayayyakin mahaifinsu da aka amince a mayar musu wanda a baya, bayan juyin mulki da akayi a ƙasar nan an karɓe kayayyaki na masu mulki bisa zargin na al’mundaha ne, amma daga baya aka wanke su gwamnatin Babangida ta ce a mayar wa kowa kayansa.
Ta ƙara da cewa sai dai su iyalan Audu Baƙo tana jin sune kawai har yanzu gwamnatn Kano data Jigawa basu gama dawo musu da kayan ba, yawanci waɗanda abin ya shafa da yake suna raye sun karɓi nasu an wuce wurin, amma su har yanzu akwai wurare da dama da ba a dawo musu da su ba. Don haka suna roƙo a dawo musu dasu domin a raba musu gadonsu don saukewa mamacin nauyi a makwanci kamar yanda malamai suka ce sai an saukewa mamaci bashi da raba gado.
Ambasada Hajiya Zainab Audu Bako ta jaddada roƙo tare da kokawa Gwamnan jihar Kano Injniya Abba Gida Gida da tace dama ya san maganar saboda haka don Allah ya kirawo lamarin duk wani abu daya rage a hannun Gwamnati na mahaifinsu marigayi Alhaji Audu Bako ya sakarwa iyalansa da sauke masa duk wani nauyi.
Shi ma marubucin littafin Kwamishina ‘yan sanda mai ritaya CP. Manya Dogo ya bayyana cewa ya rubuta littafin ne bisa lura da yayi mutane basu fahimci wanene Audu Baƙo ba shekaru da ya yi na Gwamnan jihar Kano baya barci baya hutawa saboda aiki tuƙuru, amma sai aka zo aka wofintar da shi.
Ya ce suna tare da Audu Baƙo tsawon lokaci shekara 10 dare da rana ya san abubuwa da yawa akansa irin ayyuka da ya yi a Kano babu wani Gwamna da yayi kamarsa amma sai ya ga ba a fahimce shi ba ,abin ya dame shi sosai sannan mutane basu sani ba Audu Bako yana da alaƙa da Kano mahaifiyar sa yar Mariri ce mahaifinsa ne ba daga Kano ba.
Ya ce amma duk da yadda ya kawo cigaban Kano sai ya lura daga baya ba a yabawa abinda ya yi ba ba a fahimce shi ba .Audu Bako fa a cikin ɗan lokaci ba da wani kuɗi mai yawa ba yayi Damadamai masu yawa a Kano ɗaya daga ciki ma shine Dam na biyu mafi girma a ƙasar nan kuma shi ba azzalumi bane.
Manya Dogo ya ce abinda Audu Baƙo ya yi a zamanin mulkinsa a gabansa akan idonsa ya yi amma a ƙarshe bai ga an fahimce shi ko an yaba masa ba don haka yace bari ya rubuta littafin ya shaidawa duniya ga yanda yake, gashi nan a rubuce mutane na yanzu da masu zuwa gaba su san me ya yi a Kano shi yasa ya rubuta.
