NNPC ya samu ribar Naira Tiriliyan 5.4 a 2024

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya bayyana cewa, ya kammala shekarar 2024 da ribar ta kai tsabar kuɗi har Naira Tiriliyan 5.4, a wani babban ci gaban da ya nuna yadda sauye-sauyen da ake yi a kamfanin ke ƙara tasiri.

Shugaban Kamfanin, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya sanar da hakan a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja, inda ya bayyana cewa kamfanin ya samu kuɗaɗen shiga na naira tiriliyan 45.1, wanda ya nuna hauhawar kaso 88 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

A cewarsa, kuɗin rabo ga masu hannun jarin kamfanin ya kai N27.07, abin da ya nuna ƙarin kaso 64 cikin ɗari. Ya ce wannan ci gaba ya samo asali ne daga jajircewar ma’aikata da kuma ci gaba da tafiyar da sauye-sauyen da NNPCL ke yi domin cika umarnin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na gina kamfani mai ƙarfi da ke samar da ƙima ga ’yan ƙasa.

Ojulari ya ce, sauye-sauyen da ake gudanarwa sun ta’allakallƙa ne a kan gaskiya, ƙirƙire-ƙirƙire da ingantacciyar dabarun kasuwanci, tare da nufin mayar da NNPCL kamfani mai gogayya a matakin duniya, wanda zai ci gaba da samar da riba da kuma tallafawa makomar makamashi a Nijeriya da Afirka.

Ya tunatar da cewa kamfanin, wanda aka kafa tun 1977, ya samu sauyi na tarihi a shekarar 2022, bayan aiwatar da dokar PIA ta 2021, lamarin da ya mayar da shi cikakken kamfani mai zaman kansa da ke gudanar da ayyukansa domin riba.

Ojulari ya ce, NNPCL na taka muhimmiyar rawa daga haƙo man fetur har zuwa tacewa da rarrabawa, kuma yana da tasiri wajen tabbatar da tsaron makamashi a gida da yankin Afirka.

A cikin bayaninsa, ya ce NNPCL na hanzarta zuba hannun jari a ɓangaren haƙo mai, bututun gas da makamashi mai tsafta, domin tabbatar da ci gaban da zai zarce shekaru masu zuwa. 

Daga cikin abubuwan da kamfanin ya sanya gaba akwai: ƙara haƙo ɗanyen mai zuwa ganguna miliyan biyu a rana nan da 2027, da ganguna miliyan uku nan da 2030, ƙara samar da gas zuwa billion cubic feet 10 a rana nan da 2027, da 12 nan da 2030, kammala manyan ayyukan bututun gas irin su AKK, ELPS da OB3 domin ƙarfafa samarwa a cikin gida da haɗin kai a yankin.

Tun bayan fara aiki na matatar Dangote, masana kasuwa sun ce gasa da ta kunno kai tsakaninta da NNPCL na haifar da ingantacciyar farashi da tsari mai kyau a kasuwar mai.

By ukarofi