Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani limamin cocin Katolika da ke ƙasar Birtaniya, Nick Donnelly, ya buƙaci Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da ta fitar da sammacin kama malamin addinin Musulunci na Nijeriya, Sheikh Ahmad Gumi, bisa zargin nuna ra’ayin tausayawa ga ’yan bindiga.
Donnelly ya yi wannan kira ne a shafinsa na ɗ a ranar Litinin, yana mai mayar da martani ga sabbin kalaman da Sheikh Gumi ya yi, inda ya musanta zargin cewa ana gudanar da kisan kiyashi kan Kiristoci a Nijeriya.
A wani faifan bidiyo da ya bazu, Gumi ya ce “Makiyaya ba su kama da ’yan IPOB; suna dai sace yara don neman kuɗi. Mu yi musu adalci.”
Wannan furuci ya jawo cece-kuce sosai, inda Rev. Donnelly ya ce dole ne Gumi ya fuskanci hukunci a gaban kotun ƙasa-da-ƙasa bisa zargin aikata laifukan cin zarafin ’yan Adam.
Limamin ya rubuta cewa: “Gumi na goyon bayan ‘’yan bindiga’, wato ‘yan ta’adda, waɗanda ke sace yara don samun kuɗi. Ya kamata ICC ta fitar da umarnin kama shi kan laifukan cin zarafin jama’a. Ya dace a gurfanar da shi a Hague.”
Batun zargin kisan kiyashin Kiristoci dai ya sake ɗaukar hankalin duniya ne bayan tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake kallon suna tauye ’yancin addini. Trump ya yi barazanar tura sojojin Amurka idan gwamnati ba ta daƙile kisan Kiristoci ba.
Sheikh Gumi dai ya shahara da tattaunawa da ’yan bindiga a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, abin da wasu ke fassara a matsayin yunƙurin shawo kan rikici. Sai dai duk da irin waɗannan tattaunawa, har yanzu ’yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a jihohin Arewa, suna kashe mutane da yin garkuwa da su.
