Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake ɗage ci gaba da shari’ar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan zargin aikata laifin yaɗa bayanan ƙarya ta hanyar intanet, inda ta sanya sabon ranar sauraron shari’ar zuwa 4 ga Fabrairu, 2026.
Wannan jinkirin ya faru ne sakamakon rashin halartar alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Mohammed Umar, a zaman da aka shirya gudanarwa ranar Litinin.
Tun da farko an ayyana ranar 4 ga Fabrairu, 2025 ne a matsayin ranar fara sauraron shari’ar, bayan jinkirin da aka sha yi a watannin baya, ciki har da ranar 21 ga Oktoba wadda shari’ar ta tsaya saboda zanga-zangar da Omoyele Sowore ya jagoranta don neman sakin Nnamdi Kanu.
A ranar 22 ga Satumba, an ɗage shari’ar zuwa 21 ga Oktoba bayan tsayawar ci gaba sakamakon ƙalubale da lauyan sanatar ya gabatar kan ikon kotu wajen sauraron ƙarar.
Sanata Natasha, wadda aka gurfanar a ranar 30 ga Yuni, tana fuskantar tuhuma shida da Ofishin Babban Lauyan Tarayya ya shigar. An bayar da belinta bayan gurfanar da ita, sannan aka tsara fara shari’ar daga baya.
Sai dai a ranar da aka shirya fara gabatar da shaidu, lauyanta, Ehiogie West-Idahosa, SAN, ya soki ci gaba da shari’ar, yana mai cewa akwai ƙarar shar’anta ikon kotu (preliminary objection) da suka riga suka shigar. Ya ce wannan ƙalubale ba ya kan nau’in tuhumar, amma kan abin da ya kira yin amfani da ikon AGF ba bisa ƙa’ida ba wajen gurfanar da sanatar.
Lauyan ya zargi masu shigar da ƙara da rashin miƙa musu bayanan shaidu, wanda hakan ke karya tsarin gudanar da shari’a. Duk da cewa lauyan gwamnati, David Kaswe, ya nemi kotun ta ci gaba da sauraron shari’ar, Mai Shari’a Umar ya dage cewa dole a fara warware ƙalubalen da lauyan sanatar ya shigar kafin komawa kan asalin tuhumar.
Abin da ake tuhumar Sanata Natasha da shi:
A cikin ƙarar da aka yiwa lamba FHC/ABJ/CR/195/2025, ana zargin Sanata Natasha da yaɗa bayanan ƙarya da na tunzura jama’a ta hanyar intanet, da nufin ɓata suna, tayar da rikici, da kuma haifar da barazana ga rayuka.
Ana zarginta da cewa a lokacin taro da ta yi a Ihima, Kogi, a ranar 4 ga Afrilu, ta yi ikirarin cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya umurci tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, da su hallakata. Ana tuhumarta da yin irin wannan kalami a wata hira ta talabijin.
Tuhumar dai ta dogara ne kan tanade-tanaden Cybercrimes Prohibition and Prevention (Amendment) Act 2024, doka da ke hukunta duk wani amfani da fasahar sadarwa wajen yaɗa bayanan da ka iya tada hankalin jama’a ko barazana ga tsaro.
Masana shari’a na ganin cewa cigaba da ɗaga shari’ar na iya jawo Dogon lokaci kafin a fara sauraron shaidu, domin kotun na son warware ƙalubalen da aka gabatar kan ikon kotun tun farko. Wannan na iya kai ga wani sabon jinkiri idan ɓangarorin sun sake gabatar da ƙarin matsalolin doka.
