Yadda Tinubu ya sa ido da kansa wajen kuɓutar da ’yan cocin Eruku 38

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An samu cikakkiyar hujja cewa Shugaba Bola Ahmad Tinubu ne da kansa ya sa ido kan dabarun da hukumomin tsaro suka gabatar, lamarin da ya kai ga nasarar kuɓutar da mambobin cocin Christ Apostolic Church na Eruku 38 da aka yi garkuwa da su a Ifelodun, jihar Kwara.

Jami’an DSS suka aiwatar da ceton cikin nasara da misalin ƙarfe 3:20 na ranar Lahadi.

Wasu ’yan bindiga da ke ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun kai mummunan farmaki a cocin ranar Laraba, inda suka buɗe wuta kan mutane, lamarin da aka yaɗa kai tsaye ta kafafen sada zumunta. Harin ya yi sanadin mutuwar mutum biyu, yayin da da dama suka jikkata. Daga nan suka tafi da mutane 38 zuwa daji, abin da ya haifar da fushi da kira daga ƙasa da duniya cewa a gaggauta ceto su.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaƙ, ya gode wa Shugaba Tinubu, Mai Baiwa Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu, Daraktan DSS Oluwatosin Ajayi, da sauran hukumomin tsaro bisa rawar da suka taka wajen ceton waɗanda aka sace. Ya ce al’ummar duniya da dama sun kwana cikin tsananin damuwa tun bayan harin.

Majiyoyin tsaro sun shaida cewa Tinubu ya kame kansa wajen karɓar rahotanni a ko wane lokaci, yana nazarin zaɓin matakan tsaro da aka gabatar masa, tare da jajircewa wajen tabbatar da cewa gwamnatinsa na kare rayukan addinai daban-daban, ciki har da Kiristoci.

A cewar majiyoyin, ɗaukar matakin da Shugaban ƙasa ya yi ya janyo gudanar da binciken leƙen asiri mai zurfi da kuma sintirin sama ta Ofishin NSA, wanda hakan ya taimaka wa jami’an DSS gano dajin Oreke Okeigbo da ke Ifelodun, inda aka gano waɗanda aka sace.

Rahoton ya nuna cewa Shugaba Tinubu ne ya amince da kai samamen Lahadi da dakarun DSS tare da Rundunar Sojan Sama, wanda ya haifar da kuɓutar da dukkan waɗanda aka ɗauke. Ba a fayyace ko masu garkuwar sun tsere ne ko an hallaka su ba, domin aikin ya kasance cikin tsananin sirri wato “highly classified”.

Wannan yanki dai ya daɗe yana fama da hare-haren ’yan bindiga — tun watan Yuni, an kai farmaki a wani kamfanin haƙar marmara, inda aka kashe ’yan sanda biyu tare da sace ma’aikata ’yan ƙasar Sin.

Daga cikin mutane 38 da aka ceci, mata 26 ne, ragowar 12 kuma maza ne. Mafi tsufa daga ciki ya na da shekaru 67, yayin da ƙaramin yaro da aka samu ya na da shekaru biyar kacal. A cikin su akwai yara masu shekaru 6, da 9, da wasu biyu masu shekaru 10, da wasu matasa kafin balaga, da ’yan mata da maza tsakanin shekaru 20 zuwa 58.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamna, Rafiu Ajakaye, ya fitar, Gwamna Abdulrazaƙ ya yaba da yadda Shugaba Tinubu ya dakatar da tafiyarsa taron G20 a Afirka ta Kudu domin kula da matsalolin tsaro da suka shafi Kwara da Kebbi. Ya ce hakan ya nuna jajircewarsa wajen kare rayukan ’yan Nijeriya.

Gwamnan ya gode wa ofishin NSA, DSS, Sojojin Nijeriya, Hukumar NIA, da ’yan sanda, musamman sabbin tawagogin da aka tura Kwara bisa umarnin shugaban. Ya kuma jinjinawa manyan al’umma, malamai, da jama’ar Kwara bisa goyon baya da addu’o’in da suka yi tun bayan faruwar lamarin.

By ukarofi