’Yan sanda sun haramta amfani da ‘knockout’ yayin bikin shigowar sabuwar shekara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da ake tunkarar lokutan bukukuwan ƙarshen shekara, Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja ta fitar da sabuwar gargaɗi ga mazauna birnin cewa su guji saye ko sayarwa, balle amfani da bangar knockout, da sauran abubuwan fashewa masu ƙara.

Wannan gargaɗin na zuwa ne bisa tsoron da rundunar ke nunawa kan yadda irin waɗannan abubuwan ke ƙaruwa a kasuwanni da unguwanni a babban birnin tarayya.

A cikin wata takardar manema labarai da Kakakin Rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a Abuja, rundunar ta ce akwai ƙarin damuwa game da yaɗuwar abubuwan fashewa, musamman ganin yadda ake shiga lokacin bukukuwa da ke sa yara da matasa amfani da su ba tare da kulawa ba.

Rundunar ta bayyana cewa knockout da sauran nau’ukan banga ba wai abin nishaɗi ba ne kaɗai, suna iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jama’a.

Sun ce irin waɗannan abubuwan na haifar da ƙonewa, raunuka, haddasa gobara a gidaje, da kuma barazana ga rayuwar yara da tsofaffi.

Haka kuma, hayaniyar fashewar na iya jawo ruɗani har ma ya ba ’yan ta’adda ko ɓarayi damar ɓoye aikace-aikacen su a lokacin da mutane suka ruɗe da ƙarar fashewar.

A cewar rundunar, amfani da waɗannan abubuwan a lokutan bukukuwa ya saɓa wa dokokin kare zaman lafiya, kuma yana iya kawo tashin hankali a yankuna masu cunkoso. Saboda haka, an umarci duka jami’an hukumar da su tabbatar da aiwatar da dokar – inda duk wanda aka samu yana sayarwa ko amfani da su za a kama shi, a gurfanar da shi a kotu.

Rundunar ta kuma shawarci jama’a da su kasance cikin shiri, su kasance masu saka ido a unguwanninsu, tare da hanzarta sanar da jami’an tsaro duk wani da suka gani yana sayarwa ko amfani da irin waɗannan abubuwan fashewa ba bisa ƙa’ida ba.

Ta ce, duk wani rahoto ana iya kai shi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ta layukan gaggawa na ‘Yan Sandan Abuja kamar haka: 08032003913 ko 08068587311.

By ukarofi