Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarni ga Hukumar ’Yan Sanda ta ƙasa da ta fara ɗaukar sababbin jami’ai kimanin 30,000, a wani babban mataki na ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane da suka ƙaru a makonnin baya-bayan nan.
Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma ke ci gaba da fuskantar matsanancin tashin hankali sakamakon hare-haren ’yan bindiga musamman a jihohin Neja, Katsina, Kebbi, Kaduna da Filato — wuraren da rikicin garkuwa da mutane ya zama ruwan dare.
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa sabon tsarin zai bai wa hukumar damar cike gibin jami’an tsaro da ake fama da shi, tare da fitar da ƙarin jami’ai zuwa yankunan karkara da makarantu – wuraren da suka fi fama da hare-hare.
A cewar sanarwar, shugaban ƙasa ya kuma bayar da umarnin cewa duk jami’an tsaron da ke aiki wajen kula da manya masu faɗa aji (VIPs) a faɗin ƙasar a janye su daga irin wannan aiki, a mayar da su fagen aikinsu na asali – kare rayukan talakawa da dukiyoyinsu.
Ganin yadda hare-hare suka tsananta, masana harkar tsaro sun ce irin wannan sauyi yana nuna cewa gwamnati ta fara doke inda matsalar take, domin an daɗe ana zargin cewa yawan jami’an tsaro na yi wa manya aiki ya bar talakawa ba kariya.
Rahoton farko ya nuna cewa fiye da ɗalibai 300 aka sace daga makarantar sakandire ta St. Mary, da ke jihar Neja a farkon makon nan — lamari da ya sake tayar da tarzoma a faɗin ƙasar.
Sai dai cikin alheri, yara 50 daga cikin waɗanda aka sace sun samu kuɓuta, lamarin da ya faru sakamakon matsin lambar da dakarun tsaro suka yi bayan kiran gaggawa da iyayensu da gwamnatin jihar suka yi.
Wannan ba shi ne karo na farko da makarantu ke fuskantar hare-hare a yankin Arewa ba. A shekarun baya, an sace ɗalibai mata Chibok a Borno, sai kuma Dapchi da Kagara, waɗanda duk sun jawo martani daga cikin gida da na ƙasashen waje. A yau ma hare-haren suna ci gaba da sake dawowa a lokuta daban-daban.
Masu nazari sun ce, ƙarancin jami’an tsaro, rashin kayan aiki da tsananin yacuwar garkuwa da mutane na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ya sa gwamnati ta tunkari wannan sabuwar hanya ta ɗaukar ma’aikata da yawa lokaci guda.
Wasu manyan jami’an rundunar ’yan sanda sun ce ɗaukar 30,000 zai taimaka wajen sake zama da karfi a yankunan da aka rarrabe su, musamman wuraren da ake da fitattun dazuka kamar Birnin Gwari, Kontagora, Lapai, da yankin Madalla–Kwali.
