’Yan siyasa ke ɗaukar nauyin sace-sacen mutane don gurgunta gwamnatin Tinubu – Kalu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Jihar Abiya kuma sanata yanzu, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa hare-haren kisa, garkuwa da mutane da tashe-tashen hankula da ake fama da su a sassa daban-daban na Nijeriya ba haka nan kawai suke faruwa ba, sai dai tsarin siyasa da wasu ke amfani da shi domin tarwatsa mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A tattaunawarsa a shirin Sunday Politics na gidan talbijin na Channels, Kalu ya ce akwai ’yan siyasa da ke ɗaukar nauyin ’yan ta’adda da ’yan bindiga domin lalata zaman lafiya da kuma gurgunta gwamnatin Tinubu — abin da ya ce ya yi kama da dabarar da aka yi amfani da ita a lokacin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Ya bayyana cewa, waɗannan mutane na ciki da na waje suna son a jefa ƙasar cikin ruɗani, suna ƙirƙirar matsalolin tsaro domin nuna gwamnati ta gaza. Duk da haka, bai faɗi sunayen waɗanda yake zargi ba.

Kalu ya ce, irin waɗannan hare-hare “kan taso ne a duk lokacin da ake shirye-shiryen zaɓe”, inda wasu suke matsa wa gwamnati ta hanyar tayar da tarzomar da ba ta dace ba. Ya tuna cewa a zamanin Jonathan ma an sha irin wannan salo.

A cewarsa, akwai “miyagu daga cikin ƙasa da kuma wasu ƙungiyoyin duniya” da ke haɗa kai da ‘yan siyasa domin tayar da tarzoma da garkuwa da mutane, tare da lalata tsarin tsaro.

Sai dai ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya nuna cewa ya shirya tsaf wajen fuskantar ƙalubalen tsaro, yana mai cewa: “A karon farko tun bayan hawansa, ka ga yadda ya soke duk wasu ayyuka a waje domin maida hankali kan batun tsaron gida.”

Ya yi imanin cewa waɗanda aka yi garkuwa da su za a kuɓutar da su nan ba da jimawa ba, yana mai cewa jami’an tsaro sun shiga aiki ba ƙaƙƙautawa sakamakon matsin lamba da maganganun da ake yi na cikin gida da na ƙasashen waje game da rashin tsaro.

Kalu ya danganta ɗaga kai na hare-hare da wani furuci na Shugaban Amurka Donald Trump a watannin baya, inda ya yi magana kan kashe-kashe a Nijeriya. A cewarsa, maganganun Trump da kuma kamfen na 2027 da wasu suka fara tun yanzu suna ƙara zuga yanayin siyasa.

Sanatan ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗannan ‘yan bindiga “gawurtattun miyagu ne da aka saya” domin ƙoƙarin kakkaɓe gwamnatin da, a cewarsa, ke shirin gyara tattalin arziki. Ya ce waɗanda suke ɗaukar nauyin waɗannan ayyuka “ba wai rikicin addini ko ƙabilanci suke nema ba — siyasa suke yi.”

Da aka tambaye shi ko Shugaba Tinubu na da cikakkiyar masaniya kan wannan, Kalu ya ce shugaban ƙasa “yana da isasshen rahoton sirri kan duk abin da ke faruwa.”

Ya bayyana soke ɗaukar bai wa manyan mutane da ‘yan sanda da Tinubu ya yi a baya-bayan nan a matsayin matakin da ya dace, yana mai cewa matakin zai ƙara wa jami’an tsaro muhimmiyar damar mayar da hankali kan kariyar jama’a.

A ƙarshe, Orji Kalu ya ce Nijeriya na buƙatar muhimmiyar haɗin kai da Amurka wajen magance matsalolin tsaro, yana mai cewa duk wani tsoma bakin Trump zai fi amfani idan an yi shi bayan tuntuɓar gwamnatin Nijeriya.

By ukarofi