Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
An bayyana cewa shirya taron baje kolin abincin gargajiya da na zamani, tare da nune-nunen al’adun jihohin Arewa 19, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Shahuda Muhammad — Shugabar ƙungiyar ta ƙasa — da Dakta Zubaida Ahmad Nagi — Shugabar ƙungiyar ta Jihar Kano — zai kawo sauyi mai fa’ida a tsakanin matan Arewa da na Nijeriya baki ɗaya. Magajiyar Zangon Daura, Hajiya Jamila Buhari Sani, ta bayyana hakan a taron da ya gudana a Kano a makon da ya gabata. Ta yaba wa dukkan mahalarta taron kan fasahar da suka nuna wajen kawo abinci iri-iri na zamani da na gargajiya, da kuma nune-nunen al’adun Arewa. Tun da farko a jawabinta, Shugabar ƙungiyar matan Arewa ta ƙasa, Hajiya Shahuda Muhammad, ta ce an shirya taron ne domin bunƙasa kasuwanci, al’adu, da haɗa kan matan Arewa, tare da kawar da talauci a tsakaninsu. A cewarta, ‘‘kwalliya ta biya kuɗin sabulu’’ ganin yadda taron ya gudana cikin nasara. Dakta Zubaida Ahmad Nagi ta bayyana cewa daruruwan kamfanoni daga jihohin Arewa 19 sun halarci taron don baje kolin fasaharsu. Haka kuma shugabannin cibiyoyin sarrafa abinci da dama sun gabatar da jawabai game da yadda suke horar da matasa mata da kuma ɗaukar su aiki a cibiyoyinsu. ɗaya daga cikin masu jawabi, Hajiya Sakina Rabi’u Goga, wadda ta shahara a sana’ar tsire, ta ce matan sun kwace wa maza wannan sana’a domin ita kaɗai tana sayar da tsire tsinke 500 a kullum. Sauran sun haɗa da Mami Garo, Hafsat Samira, Khadija Lawan, Sadiya Hashim Sabo, Hussaina Abbas Yahaya da sauran mata masu sana’o’in abinci da suka yi jawabi a taron Arewa Festival Carnival Food. A ƙarshe, fitaccen ɗan wasan Kannywood, Umar Gombe, ya yi addu’ar zaman lafiya ga Arewa da Nijeriya baki ɗaya.
