Rukunonin makarantun Gidauniyar Isyaka Rabi’u ta yaye ɗalibai 250 

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano 

Makarantar firamare da sakandare da ke ƙarƙashin Gidauniyar Khalifa Isyaka Rabi’u Khadimul ƙur’an ta yaye ɗalibai sama da 250, kamar yadda Babban Jami’in kula da rukunonin makarantun kuma Mataimakin Darakta na mamallakin Jami’ar Khairun ADPO, Malam Rabi’u Shamma, ya bayyana yayin bikin raba kyaututtuka da jawabai da aka gudanar a harabar jami’ar da ke Kano a ƙarshen makon nan. Malam Rabi’u Shamma ya yaba wa ma’aikatan gidauniyar da masu kula da makarantun kan yadda suke aiki da himma. Haka kuma ya jinjinawa ɗaliban da iyayensu da sauran baki da suka halarci taron muhimmanci. A nasa jawabin, ɗaya daga cikin manyan baki, Ambasada Tasi’u Abdurrahman — tsohon ɗan takarar Gwamnan Kano kuma Shugaban Hajiya Halima College of Education — ya yaba da yadda ɗaliban suka nuna ƙwarewa ta ilimi, musamman kan sarrafa harshen Larabci, Hausa da Turanci. Ya ce hakan na nuna bajintar malamai da kuma ɗalibai. Daga nan ya shawarci makarantu — na gwamnati da na al’umma — su fifita koyar da sana’o’i fiye da dogaro da turanci kaɗai, yana mai kawo misalin yadda mutanen Karamar Hukumar Shanono suka dage wajen koyar da ’ya’yansu sana’o’in zamani da na gargajiya. Shi ma Alhaji Bashir Khalifa Isyaka Rabi’u (Khadimul ƙur’an) ya bayyana mamakinsa da farin cikinsa kan yadda ɗaliban gidauniyar suka kware wajen sarrafa harsuna da karatun Al-ƙur’ani. Ya gode bisa girmamawar da aka yi masa a taron. Tun da farko a jawabinta, Darakta a Hukumar Kula da Albarkatun Ilimi ta Jihar Kano (KERD), Hajiya Rabi Inuwa Hussaini, wadda ta wakilci Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta bayyana cewa wannan makaranta ta yi daidai da hangen nesa da aikin da gwamnan ke son gani a rayuwarsa. Ta ce gwamnati tana ba wa ilimi muhimmanci a kasafinta, kuma duk wata nasara da ake samu a ma’aikatar ilimi ko KERD aiki ne na Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, yayin da kwamishina Gwani Ali Haruna Makoɗa da ita wakiliyarsa ke taimaka masa wajen ganin ilimi ya ci gaba a jihar.

By ukarofi