
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Ƙungiyar Mashawartan Arewa (ACF), Bashir Ɗalhatu, ya kirayi Gwamnatin Tarayya da ta haɗa tattaunawa da ƙarfin sojoji wajen magance matsalolin tsaro a Nijeriya, yana mai cewa amfani da tsarin salo biyu ya taimaka wajen samar kyawawan sakamako a wasu sassan ƙasar.
A wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a, Ɗalhatu ya bayyana cewa salo irin na shirin yafiyarl ga ƴan Neja-Delta da aka yi a baya abu n ai matuƙar ga kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a Arewacin Nijeriya.
Ya ce, da dama daga cikin ƴan bindiga ba su da damarmakin samun ilimi da sauran ababen more rayuwa, yana kira ga gwamnatin da samar da hanyoyin janyo su a jiki ta hanyar samar musu da waɗanda ababe a lokacin da take cigaba da kiyaye hukunci mai tsauri ga aikata manyan laifuka.
A cewarsa, ana cigaba da tayar da hazo na mahawara tsakanin waɗanda ke goyon bayan amfani da ƙarfin soja kaɗai wajen magance matsalar da masu kira ga yin tattaunawar sulhu.
Saidai, Shugaban ma ACF yana bada shawarar amfani da duka biyun yayin tunkarar matsalar, sa oda yadda aka ga tasirin hakan a baya.
Ya bada misali da shirin yafiyar ƴan Neja-Deltan, wanda a sanadiyyarsa an yi nasara gyaran hali ga mayaƙan ta hanyar ba su ilimin da wasu nau’ukan tallafin rayuwa.
