‘
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Yankamaye da ke cikin ƙaramar hukumar Tsanyawa a Jihar Kano, inda suka kashe wata mata tare da sace wasu mutane uku.
Daily Nigerian ta rawaito cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Asabar, lokacin da mazauna ƙauyen suka riga suka kwanta.
Majiyoyi a yankin sun shaida wa jaridar nan cewa ’yan bindigar sun ajiye babur-babur ɗinsu a wajen garin sannan suka shigo a kafa domin guje wa a gano su.
A cewar majiyoyin, ’yan bindigar sun harbe wata tsohuwa har lahira saboda ta roƙe su kada su tafi da ɗanta.
“Sun kashe tsohuwar ne saboda ta roƙe su kada su tafi da ɗanta. Sai suka harbe ta suka tafi da ɗan nata.
“Daga nan kuma suka shiga wani gida suka sace mata biyu, ciki har da surukar kansilan yankin,” in ji wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa.
Rundunar ’yan sanda ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba tukuna.
Ƙauyen Yankamaye, wanda ke kimanin kilomita biyar daga garin Rimaye a Jihar Katsina, na fama da hare-haren ’yan bindiga tun bayan da wasu al’ummomin Katsina suka rattaba hannu kan yarjejeniyar “sulhu” da su.
Kazalika, ƙauyukan makwabtaka kamar Sundu da Buresawa suma na fama da irin waɗannan hare-hare a kwanakin baya-bayan nan.
Sannan a kalla mutane takwas aka sace a wani hari da aka kai Biresawa da daddare a ranar Litinin da ta gabata.
