Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinan ayyuka, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya bayyana cewa titin mai tsawon kilomita 27.6 zai fara ne daga cikin garin Sabuwa ya bi ta Mazare har zuwa Tashar Bawa a ƙaramar hukumar Sabuwa.
Injiniya Magaji yayi wannan magana ne lokacin da gwamna Dikko Raɗɗa ke shirin ƙaddamar da aikin hanyar.
Ya ce, idan an kammala aikin zai taimaka wajen bunƙasa tsaro, sauƙaƙa jigilar amfanin gona da harkokin sufuri, tare da farfado da tattalin arzikin yankin.
Wakilin Sabuwa a Majalisar Dokoki, Hon. Ibrahim Danjuma Macika, ya jinjina wa gwamna bisa wannan aikin, haka ma Shugaban ƙaramar hukumar Sabuwa, Engr. Sagir Tanimu, wanda ya bayyana aikin hanyar a matsayin wani abin cigaban da ba su taɓa gani ba.
Shugaban kamfanin da zai aiwatar da aikin, Fullman Construction Company Ltd, Alh. A. A. Albasu, ya tabbatar da cewa za su yi aiki mai inganci kuma cikin wa’adin da aka tsara.
Kamar yadda ake yi a kowace ƙaramar hukuma, a Sabuwa gwamna Raɗɗa ya ziyarci hedikwatar ƙaramar hukumar domin ƙaddamar da shirin bada tallafi na miliyoyin naira da shugaban ƙaramar hukumar tare da wasu masu kishin yankin suka samar. Haka kuma ya buɗe wasu muhimman ayyuka da shugaban ƙaramar hukumar ya aiwatar, sannan ya gana da masu ruwa da tsaki domin tattauna cigaban al’umma da siyasar yankin.
Ya kuma kai ziyarar ban girma ga Sarkin Kogin Hakimin Sabuwa inda hakimin ya yaba wa Gwamna Raɗɗa kan yadda ta tunkari harkokin tsaro a jihar musamman a ƙaramar hukumar Sabuwa.
Haka ma Kogunan Katsina ya yaba wa gwamnan bisa yadda ya ke kawo ayyukan cigaba a birane da karkara karkashin shirin cigaban al’umma CDP.
Dikko Raɗɗa ya kuma ziyarci wasu muhimman wuraren gwamnatin inda ya ya nuna rashin jin daɗin sa ga yadda yaga wata makarantar firamare a lalace “nan take ya bada izinin aje a yi mata duk gyaran da take bukata.
Daga nan gwamna ya wuce sabuwar makarantar da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kankara, Faskari da Sabuwa, Rt. Hon. Dalhatu Tafoki, ya samar, inda gwamnan ya kafa tubalin fara aikin ginin.
Gwamna Raɗɗa ya samu rakiyar jami’an gwamnati da su Sanatan Katsina ta Kudu, Sen. Muntari Dandutse, Hon. Jabir Tsauri, Shugaban Jam’iyyar APC na jiha, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, kwamishinoni, wakilan al’umma.
