Jonathan ya ba Tinubu ba’asin juyin mulkin Guinea-Bissau a Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya bayyana masa ainihin halin da ake ciki a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin da ya gudana a ƙasar.

Jonathan, wanda ya jagoranci tawagar West African Elders Forum (WAEF) zuwa ƙasar a matsayin mai sa ido kan zaɓen ƙasar, ya ce lamarin da ya faru ba kawai rikicin siyasa ba ne, illa wani abin da ya kira “ceremonial coup”, wato juyin mulki mai kama da na doka amma wanda bai bi tsarin dimukraɗiyya ba.

Ya ce, rundunar soji ta Guinea-Bissau ta katse tsarin tattara sakamakon zaɓe, ta rufe iyakokin ƙasa, sannan ta kama wasu shugabannin adawa, lamarin da ya jefa ƙasar cikin rikici da rashin tabbas.

Ya faɗa wa Shugaba Tinubu cewa ECOWAS na buƙatar shiga tsakani cikin gaggawa domin tabbatar da an dawo da tsarin mulki da sako waɗanda aka kama, kuma a bayyana wanda ya ci zaɓen da aka kusa kammalawa kafin juyin mulkin ya faru.

Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta yarda da duk wani salo na karɓar mulki ta hanyar da ta sabawa tsarin dimukraɗiyya ba, tare da nanata buƙatar ECOWAS da AU ta su matsa lamba don dawo da zaman lafiya da adalci a ƙasar.

A cewar Jonathan, rikicin ka iya haifar da illa ga yankin Yammacin Afirka matuƙar ba a tunkare shi da gaggawa ba, duba da yawaitar juyin mulki a wasu ƙasashen nahiyar.

By Babaji