Gwamnatin Katsina za ta gina hanya a kan Naira biliyan 18.5 a Sabuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin gina hanya mai tsawon kilomita 27.5 daga sabuwa zuwa Rafin Iwa a ƙaramar hukumar Sabuwa.

Aikin hanyar da zai ci kuɗi Naira biliyan 18.5 za a kammala shi a nan da watanni 18 kuma da idan an kammala zai haɗa ƙauyuka 50 waɗanda al’ummar su duk manoma ne da zai taimaka masu wajan safarar kayan abinci.

Da yake jawabi bayan ƙaddamar da aikin hanya gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewar fara aikin daga cikin alkawarin da yayi a lokacin yana yaƙin neman zaɓe musamman gina hanyoyi a karkara da zai taimaka wa manoma su sami sauƙin sarrafa amfanin gonar su.

A yayin da gwamnan ya hori ɗan kwangilar da gudanar da ingantaccen aiki kuma akan lokaci kamar yadda akai yarjejeniya,ya kuma yi kira da al’ummar yankin da suba ɗan kwangilar da Injiniyoyi na ma’aikatan ayyuka haɗin kai domin a sami nasarar kammala aikin ba tare da wani cikas ba.

A jawabinsa Kwamishina ayyuka da gidaje Injiniya Sani Magaji Ingawa ya sanar da cewa gwamnati ta biya shi kashi 40 bisa ɗari na kuɗin aikin da yanzu haka a fara kai kayan aiki a wurin.

Ya tabbatar wa manoma da filayen da aikin hanyar ya shafa gwamnatin za ta biya su diyya,domin har shima yayi kira ga al’ummar yankin da su bada haɗin kai da goyon baya domin samun nasarar aikin.

Shima shugaban ƙaramar hukumar Sabuwa godewa gwamna Dikko Raɗɗa ya yi kan bada aikin wannan hanya da aiwatar da wasu manyan ayyuka a ƙaramar hukumar da babu shakka acewar sa zai taɓa rayuwar al’ummar yankin.

By ukarofi