
Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NARD), ta sanar da dakatar da yajin aikin gama gari bayan shafe kwanaki 29 tana yi sakamakon cimma matsaya da Gwamnatin Tarayya.
NARD ta dakatar da yajin aikin ne biyo bayan tattaunawa da aka yi a taron gaggawa na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar.
Sakatare Janar ɗinta, Dakta Shuaibu Ibrahim ne ya tabbatar da haka a wata tattaunawar waya da manema labarai.
Ya ce, an cimma wannan matsaya ne bayan da ƙungiyar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da Gwamnatin Tarayya kan muhimman buƙatu guda bakwai da likitocin suka gabatar.
Yajin aikin wanda ya jefa harkokin lafiya cikin matsin lamba a faɗin ƙasar, inda kimanin likitoci mazauna 11,000 a asibitocin koyarwa 91 suka janye daga aikinsu sakamakon rashin kyawun yanayin aiki da kuma bashin kuɗaɗen.
Dakta Ibrahim ya bayyana cewa daga cikin buƙatun bakwai da aka gabatar, guda biyu tuni aka cika su.
Waɗanda suka haɗa da sakin teburin ‘Professional Allowance’ da kuma bayar da umarni ga matakin shigar likitoci na komawa CONMESS 3.
Sauran buƙatun da ake sa ran cika su cikin makonni huɗu sun haɗa da: sake dawo da likitocin Lokoja da aka dakatar, biyan bashin kuɗin karin girma, warware bashin albashi a wasu asibitoci, aiwatar da inganta matsayin likitocin da suka ci jarrabawar Part I, aiwatar da alawus na ƙwararru, da kuma warware matsalar takardar shaidar mambobinsu.
Amma kuma duk da haka NARD ta gargaɗi Gwamnatin Tarayya cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen komawa yajin aiki muddin aka gaza cika sauran buƙatun kafin cikar wa’adin da aka sanya a yarjejeniyar.
