Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da hanyar Zobe mai tsawon kilomita 17 da ta tashi daga Saubashi zuwa Shiye ta miƙa zuwa Munawa har Dan’aunai a ƙaramar hukumar Dutsi ta jihar Katsina.
Gwamnan jihar ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa na da cikakken niyyar faɗaɗa ci gaban karkara, ƙarfafa ayyukan jin ƙai, da inganta walwalar al’ummomi a duk faɗin jihar.
Ya bayyana haka ne a yayin ziyarar aiki da ya kai ƙaramar hukumar Dutsi, inda ya duba ayyukan ci gaban da ake gudanarwa tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar.
Gwamna Raɗɗa ya fara ziyarar ne da kaddamar da manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi guda biyu da ɗan majalisar ƙaramar hukumar Dutsi ya fara aiwatarwa.
Ayyukan hanyar kuwa akwai Sobashi zuwa Munawa har Dan’aunai da hanyar Tashar Dan’aunai Dodar da gwamnan ya ce wannan ƙoƙari zai taimaka wajen “ƙarfafa jigilar mutane da kayayyaki a karkara, buɗe al’ummomin da ke nesa, tare da farfaɗo da harkokin zamantakewa da tattalin arziki a cikin ƙaramar hukumar.”
Gwamnan ya ziyarci fadar hakimin Dutsi, inda ya bayyana mai irin muhimman ayyukan ci gaban jihar da ake gudanarwa.
Hakimin ya nuna jin daɗin sa dangane da yadda gwamnatin ke mutunta masarautu, tare da roƙon a ƙara samar da hanyoyi da kuma jaddada buƙatar samar da tsaftataccen ruwa a wasu al’ummomi.
A cikin jawabinsa, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatin sa ta ƙaddamar da hanyar cikin gari mai tsawon kilomita 3.5 da hanyar karkara mai tsawon kilomita 17 da shugaban ƙaramar hukumar ke aiwatarwa domin inganta zirga-zirga zuwa gonaki, kasuwanni da maƙwabtaka.
Ya kuma ce hanyar Ingawa zuwa Shargalle “muhimmin zuba jari ne da ya sauya al’amura, tare da inganta haɗin kai a wannan yanki.”
Game da matsalar ƙarancin ruwa kuwa, Gwamna Raɗɗa ya tabbatar wa al’ummar yankin cewa samar da ruwan sha mai tsafta na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin sa ta fi mayar da hankali a kai. Ya ce: “Za mu yi aiki tare da ƙaramar hukumar Dutsi domin samar da ingantattun hanyoyin ruwan sha a al’ummomin da suka fi fama da matsalar.”
Gwamnan ya buƙaci al’ummar ƙaramar hukumar da su cigaba da gudanar da addu’o’in samun taimakon Ubangiji kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan jihar. A cewar sa, “zaman lafiya da tsaro suna buƙatar haɗin kai, himma, da goyon bayan kowa.”
A harabar sakatariyar ƙaramar hukumar Dutsi, Gwamnan ya gudanar da taron masu ruwa da tsaki wanda ya haɗa da sarakunan gargajiya, wakilan al’umma, shugabannin siyasa da ƙungiyoyin matasa.
Shugaban ƙaramar hukumar Dutsi ya yi godiya bisa irin tallafi da goyon bayan da gwamnatin jiha ke bayarwa, ciki har da hanyar Shargalle,Ingawa da sabbin ayyukan da aka ƙaddamar.
A nan ma Gwamna Raɗɗa ya nanata cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da sauraron buƙatun jama’a tare da tsara muhimman ayyuka bisa ainihin buƙatunsu.
Ya jaddada cewa jam’iyyar APC yanzu na da manyan ayyuka a matakai daban-daban na gwamnati da za a gabatar da su ga jama’a.
