Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata ƙungiya mai zaman kanta ta ‘Citizens Participation Against Corruption Initiative’ (CPACI), ta bayyana damuwa kan kutsen ‘yan bindiga a wasu sassan Jihar Kano, tana mai cewa lamarin na barazana mai tsanani ga zaman lafiyar Arewa baki ɗaya da ginshiƙin tattalin arziƙinta.
Babban darektan ƙungiyar, Bishir Dauda Sabuwar-Unguwa Katsina, ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja.
Ya ce, samun kutsen ‘yan bindiga zuwa yankunan wasu ƙananan hukumomi da ke jihar Kano — musamman a Shanono, Bagwai da Tsanyawa — wuri da ya kira “kagarar ƙarshe da ba a iya karyatawa” a Arewa, wajibi ne ya zama babban jan kunnen hukumomin tsaro da ‘yan siyasa.
Ya jaddada cewa barin Kano, wadda ita ce jiha mafi yawan jama’a kuma cibiyar kasuwanci a Arewa, ta faɗa cikin mummunan halin ta’addanci na yiyuwar haifar da sakamako mai muni fiye da abin da ake iya hango wa a yanzu.
A cewarsa, idan Kano ta zame wa ‘yan bindiga filin wasanni, za ta iya zama jiha a gaban gaba wajen matsalar tsaro, lamarin da zai sanya Arewa ta Yamma gaba ɗaya cikin mawuyacin hali na ta’addanci da fashi da makami.
Sabuwar-Unguwa ya bayyana damuwa kan yadda wasu ‘yan siyasa ke kokarin juyar da wannan mummunan al’amari zuwa abin cin moriyar siyasa, maimakon su haɗa hannu su fuskanci barazanar gaba ɗaya.
Ya yi kira da a gaggauta binciken zarge-zargen da gwamnatin Jihar Kano ta yi cewa wasu masu ruwa da tsaki na siyasa na da hannu a yadda tsaro ke kara taɓarɓarewa a yankin.
A kalamansa, “Siyasantar da matsalar tsaro na rushe ƙoƙarin gwamnati na tinkarar masu laifi. Wannan lamari na rayuwa da mutuwa ne, kuma muna sa ran ‘yan siyasa, ba tare da la’akari da jam’iyyunsu ba, su haɗa kai da kai su fuskanci matsalar kafin ta cinye mu duka.”
Ya kuma soki batun da wasu ke yaɗawa na kafa ƙungiyoyin sintiri irin na mayaƙa a ƙarƙashin ƙara ƙarfin Hisbah, yana mai gargaɗin cewa irin wannan mataki na iya tayar da rikicin cikin gida da kuma janyo sabon salo na tashin hankali.
Sabuwar-Unguwa ya danganta hare-haren da ake samu a Kano da illa daga makwabciyar jiha, Katsina, inda a cewarsa wasu al’ummomi suka yi ƙoƙarin magance ‘yan bindiga ta hanyar yarjejeniyar sulhu ba tare da cikakken tsari ba.
Ya ce irin wannan mataki, ba tare da kulawar gwamnati, kwashe makamai ko tsare-tsaren gyara da mayar da su cikin al’umma ba, na ƙara ruruta wutar rashin tsaro a Arewa ta Yamma.
A cewarsa, “Ba zai zama abu mai ma’ana ba a ce Jibia da Batsari na jin daɗin zaman lafiya, alhali Tsanyawa da Shanono na fama da ta’addanci. Yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga ba ta aiki yadda ya kamata, kuma dole ne a sauya dabarar.”
ƙngiyar CPACI ta ba da shawarar cewa duk wata tattaunawa da ‘yan bindiga dole ta haɗa da tilasta kwace musu makamai, a shigar da su cikin shirye-shiryen gyara, sannan a dawo da su cikin al’umma ga waɗanda suka nuna nadama ta gaskiya.
Ta kuma jaddada buwatar daidaita matakan tarayya da na jihohi domin a samu manufa guda, mai sahihanci.
Ta nemi jami’an tsaro su ƙara tsananta farmakin soji a kan ‘yan bindigar da ba sa son sulhu, tare da amfani da dabarun da ba na ƙarfi ba a lokaci guda, a tsari ɗaya da ya ƙunshi dukkan matakan gwamnati.
A cewarta, sai an haɗa ƙarfi da hikima ne za a iya daƙile barazanar da ke ƙara kutsa kai cikin zuciyar Arewa.
