Ranar masu buƙata ta musamman: Nakasassu 1000 ne suka amfana da tallafi a Kebbi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Ranar 3 ga watan Disamba ita ce ranar da aka ƙayyade a matsayin ranar nakasassu ko kuma masu buƙata ta musamman ta duniya.

Jihar Kebbi ita ma ta bi sahun sauran duniya wajen bikin wannan ranar inda ta yi amfani da wannan ranar don tallafawa mutane dubu ɗaya da babura da sauran kaya na buƙatar yau da kullum a ƙarƙashin ma’aikatar ayyuka na musamman.

Kwamishina a ma’aikatar Honarabul Zayyanu Umar Aliero ya bayyana cewa ma’aikatar a cikin wani akin haɗin gwiwa da ofishin Uwargidan shugaban ƙasa suka shirya wannan tallafin ga masu buƙata ta musamman.

Ya ce an shirya wannan ne saboda su ma masu buƙata ta musamman su ji ana tare da su ba a mayar da su saniyar ware ba, su ma mutane ne kuma suna haƙƙi kan gwamnati da ya kamata ta sauke.

Ya ƙara da cewa har wa yau a cikin shirin Uwargidan shugaban ƙasa ta raba kayan sana’o’i daban-daban ga mutane ɗari biyu da hamsin (250) yayin da ita kuma gwamnatin jihar Kebbi ta raba kayan kuɗi Naira dubu dari (100,000:00) ga mutane dari shoda da hamsin (650) saboda su karfafa sana’o’i daban-daban a maimakon yawon barace-barace.

Haka-zalika har wa yau gwamnatin jihar Kebbi ta kuma raba babura masu dari daya (100) masu aiki da hasken rana wanda idan aka hada gaba ɗaya mutane dubu ɗaya suka samu tallafin.

Bayan wannan kuma Uwargidan gwamnan jihar Kebbi Hajiya Zainab Nasir (Nasare) ta bayarda gudummawar buhunan shinkafa dubu ɗaya don rabawa ga dukkan waɗanda suka samu tallafin a matsayin na ta gudummawa.

An gudanar da bikin ne a ɗakin taro na Kwalejin ƙere-ƙere na Waziri Umaru da ke garin Birnin Kebbi.

By ukarofi