Lakurawa sun sun kashe maƙerin  bindiga a Kebbi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Waɗansu mutane da ake kyautata zaton Lakurawa ne sun kai samame a kasuwar wani gari da a ke kira Amagwaro da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a ƙaramar Hukumar Arewa da ke jihar Kebbi.

Wani ganau ya bayyanawa wakilin Blueprint Manhaja da cewa waɗannan Lakurawan sun shiga kasuwar ne inda suka rinka tambayar mutane suna neman wannan mutumin ne har suka gano rumfarsa, bayan da suka tambaye shi ko shi ne ke ƙera wata bindiga (Wagila), bayan amsa daga nan sai daya daga cikin su ya zaro bindiga ya harbe shi nan take uya mutu sai suka hau baburan su suka gudu.

Ya bayyana cewa daman su ‘yan ta’addan suna jin tsoron irin wannan bindigar Wagila saboda a maimakon harsashe ana amfani da fulogi ne wanda idan aka harbi mutum ya kan tarwatse ne kuma saboda haka mutane da dama sun tanadi irin ta domin kariyar kan su da dukiyoyin su a ƙauyuka da dama.

Ya ƙara da cewa yanzu haka dai ita wannan wannan bindigar ta yawaita a hannun mutane da a duk lokacin da aka kai musu hari suna amfani da ita saboda haka waɗannan Lakurawan sun fi jin tsoron ta yana ganin wannan shi ne dalilin da ya sa suka kashe wannan mutumin.

By ukarofi