Kano: An kwaɗaitar da ƴan kasuwar Bichi sanya dabarun zamani a harkokinsu

Spread the love

Shugaban Hukumar Raya Kogin Hadejia da Jama’are, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi ya yi kira ga ‘yan kasuwar Bichi a kan mai da hankali wajen shigo da dabarun kasuwancin zamani cikin harkokin kasuwancinsu.

Ya bayyana haka, a yayin da kungiyar ƴan kasuwa ta (Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited) ta kai masa ziyara a ofishinsa dake jihar Kano.

Da ya ke jawabi, Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi, ya nuna farin ciki da jin dadin wannan ziyara, inda ya bayyana hakan a matsayin hadin kan da zai samar da cigaba mai dorewa, ya kuma kara da shawartar su game da koyon hanyoyin lissafi da kididdiga a cikin kasuwancin nasu na yau da kullum tare da janyo matasa cikin harkokin kasuwancin, domin dorewar cigaba da bunkasa kasuwanci a karamar hukumar baki daya.

Alhaji Rabi’u Sulaiman, ya kara da cewa kofarsa a bude take a duk lokacin da ‘yan kasuwar ke bukatar wani abu na cigaba a bangarensa, inda daga bisani ya yi fatan alheri da samun nasarar cigaba mai dorewa ga ‘yan kasuwar da ma kasuwar baki daya.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Abubakar Mazahimu Sale ya bayyana, kungiyar ta nuna farin ciki da jin dadi bisa yadda shugaban hukumar da ma’aikatansa suka tarbe su, inda tun da fari shugaban na ‘yan kasuwar ya bayyana manufar ziyarar tasu da cewa, sun je ne domin girmamawa da neman shawarwari da nasiha, kasancewar shugaban, tsohon dankasuwa da ya fara kasuwanci tun daga tushe, har ya kai matsayin babban dan kasuwa a kasar nan.

A nasa jawabin Shugaban Kwamitin Dattawa na kasuwar, Alhaji Lawan Ibrahim, ya bayyana Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi a matsayin mai kishi da kawo cigaba a Karamar Hukumar Bichi, duba da ayyukan alheri da ya kawo na gina Dam din Bela, da Malikawa-Garu da kuma garin Kungu, kamar yadda jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta ruwaito.

By Babaji