An yaba wa Kwankwaso bisa zama ginshiƙin NNPP a Kano

Spread the love

An jinjina wa jagoran Kwankasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso kan zama tushe na samar da gwamnatin alheri ga jama’ar Kano.

A wata sanarwar da Jami’ar Yada Labarai ta Ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, Mataimakin Shugaban Hukumar Yawon Bude Idanu ta Jihar Kano, Alhaji Tijjani Aliyu ne ya yi jinjinar da godiya a yayin gudanar da taron zaɓen shugabanin Jam’iyyar NNPP na Bichi a Cibiyar Musulunci dake yankin.

A jawabinsa, Alhaji Tijjani Aliyu, ya nuna jin daɗi game da zaman lafiya da haɗin kai da jam’iyyar tasu ta NNPP ta ciri tuta a kai, duba da irin dimbun ayyukan gina al’uma da Gwamnatin injinya Abba Kabir Yusuf ke gudanarwa a fadin jihar Kano.

“Muna godiya ga jagora Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, duk abubuwan alhetin da Gwamnatin Kano ke yi shi ne ya assasa su, kuma muna godiya ga mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf da yake ta ayyuka ba ji ba gani ba dare ba rana, wanda mutum ko hasidin iza hasada ne, yau idan ya shigo Kano ya san ana aiki.”

Ɗaya daga wakilan hedikwatar jam’iyyar a matakin jiha da aka tura domin kula da yadda karamar hukumar za ta gudanar da zaben, Alhaji Zaharadden Ibrahim, ya yi bayanin yadda yakamata tsarin zaben zai kasance kamar yadda yake bisa jagoranci na jam’iyyar.

“Dukkan shugabannin da suka rike a baya ba a yarda a sauya su ba, idan ba tare da wata matssla ba; ko dai a ce mutum ya mutu ko kuma a’a ya bar jam’iyyarmu ta NNPP mai albarka, ko kuma ya samu wani muƙami daga ƙaramar hukuma, to jam’iyya ta ce, wajibi ne a ba shi zabi ya dauki irin matsayin da yake so.”

A nasa ɓangaren, Daraktan Ƙananan Masana’antu, Kasuwanci da Talla, Abubakar Ahmad Bichi, ya jaddada cewa matasan yankin har wa yau suna nan tare da wannan gwamnati dari bisa dari, sakamakon ayyukan alheri da take assasawa kodayaushe, inda a ƙarshe ya yaba wa shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata.

“Wannan zaɓe da aka tabbatar da Alhaji Hamza Sule Mai Fata a matsayin shugaban karamar hukuma, wanda ko wane ne kai a wannan jiha tamu mai albarka ka san cewa Kwalliya ta biya kudin sabulu.”

Shugabannin Jam’iyyar NNPP na yankin dai su ne; Shugaban Jam’iyya Aminu Muhammad da mukaddashi da mataikansa uku, sai Sakatare Abubakar Garba da Ma’aji Usman Magaji Ɗan-Zabuwa, Jami’in hulda da Jama’a kuma Annur Toni da dai sauran tawagar masu rike da muƙaman jam’iyyar a matakin Ƙaramar Hukumar.

Haka kuma, taron ya haɗa da Muzammilu Yusuf wakili daga matakin jiha da Baturiyar Zaɓe ta Ƙaramar Hukumar da kuma ɗimbin mabiya jam’iyyar na yankin ciki har da sakataren kokas na jam’iyyar NNPP Bichi, Ahmad Haruna, wanda kuma yake ɗaya daga cikin ƴan kwamitin da suka shirya zaɓen.

By Babaji