Kano: An gargaɗi jagororin kasuwa a Bichi akan kiyaye jagoranci na gari

Spread the love

Alkalin Kotun Shari’ar Muslunci ta Ƙaramar Hukumar Bichi, Malam Mubarak Ado Abdullahi ne ya yi wannan jan hankalin a yayin da ƙungiyar ƴan kasuwa ta (Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited) ta kai masa ziyara a unguwar Buden Gari.

Da yake jawabi, Mai Shari’a Mubarak Ado Abdullahi, ya nuna jin daɗin wannan ziyara mai dorar da hadin-kai.

Mai Shariar wanda ya yaba wa ƙungiyar bisa ƙoƙarinta na daƙile dukkan wata ɓarna acikin kasuwar ya hore su da su zama masu sa ido game da abubuwan da ake sayarwa acikin kasuwar.

Tun da fari shugaban ‘yan kasuwar, Alhaji Abubakar Mazahimu Sale, ya bayyana manufar ziyarar tasu, inda ya ce sun ta ne musamman don girmamawa da kuma neman shawarwarin alƙalin kotun.

A nasa ɓangaren Magatakardan Kotun mai Kula da Ɓangaren Kudi, Malam Aminu Kabiru, ya yi kira ga ‘yan kasuwar dangane da ƙarfafa aikin Kwamitin Dattawa na Kasuwar, wajen gabatar da sulhu da sasanci a tsakanin ƴan kungiyar, tare da samar da ofishin kula da haƙƙin masu sayan kaya, waɗanda sune suke da alhakin kula da masu ƙorafi ta ɓangaren abokan kasuwanci.

A ƙarshe Magatakardar Kotun mai Kula da Bangaran Gudanarwa, Malam Gaddafi Kabiru Abubakar Bichi, ya yi addua da fatan samun nasara da cigaba mai ɗorewa ga ‘yan kasuwar da ma kasuwar baki ɗaya, kamar yadda Jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta ruwaito.

By Babaji