Ɓatanci: Akpabio ya shigar da ƙarar neman biyan sa biliyan N200 akan Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya maka Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ƙara a kotu akan zargin ɓata masa suna, yana mai neman ta biya shi diyyar Naira biliyan 200.

Sanata Natasha mai wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya, ta tabbatar da karɓar sammacin a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna jin daɗinta tana mai cewa ta samu damar bayyana hujjojinta akan zargin yunƙurin lalata da ta zarge shi da yi da ita a baya.

“Yau 5 ga watan Disamban 2025, na karɓi sabon sammacin kotu kan ƙarar diyya ta naira biliyan 200 da Sanata Godswill Akpabio ya kai ni game da ɓata masa suna da zargin lalata”, a cewar Natasha.

“Na yi farin ciki da Sanata Akpabio ya taso da wannan batu saboda kwamatin ɗa’a na majalisa ya ƙi amincewa ya saurare ni kan batun sakamakon matar Akpabio ta shigar da ni ƙara a kotu.”

A watan Fabrairun 2025 ne Natasha ta zargi Akpabio da neman yin lalata da ita bayan rikicin da ya ɓarke a tsakaninsu, wanda ya kai ga dakatar da ita daga zaman majalisar na tsawon wata shida.

Akpabio, wanda kuma tsohon gwamnan Akwa-Ibom ne, yana neman kotu ta tilasta wa Sanatar biyansa wasu maƙudan kuɗaɗe na zargin ɓata masa suna da kuma bada haƙuri a gidajen jaridu na ƙasa.

By Babaji