Gwamnatin Katsina za ta kafa masana’antar sarrafa garin kwaki a Batsari

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a sakatariyar ƙaramar hukumar Batsari a cigaba da ziyarar aiki da yake kaiwa a ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.

Ya ce gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne ganin yadda garin Wajibi da babu wanda yafi su noman rogo a jihar suna shanya rogon a bakin hanya.

Garin Wajibi shima mafi girma a ƙaramar hukumar Batsari bayan garin na Batsari.

Haka kuma gwamnan yace gwamnatin jihar za ta gina makarantun ƙanana da manyan sakandire guda biyar a jihar.

Dikko Raɗɗa ya ce zuwan su Batsari ya tabbatar da zaman lafiya ya samu”shi yasa muka zo mu jajanta maku,mu kuma taya ku murnar samun zaman lafiya,”inji Raɗɗa.

Gwamnan ya bayyana cewa mazaɓu 6652 da ke jihar babu inda ba a kai aikin bunƙasa ƙasa ba.

Da ya juya kan ƙaramar hukumar Batsari,gwamna Dikko Raɗɗa ya tabbatar da cewa gwamnatin a yanzu ta sakarwa ƙananan hukumomi mara “Muna sakar masu da kuɗaɗen su gaba-daya a duk wata.

“Yanzu haka na ƙaddamar da aikin hanya da karamar hukumar ke aiwatar da na miliyoyin Naira a mayan garuruwan Batsari da Wagini.

Tunda farko a jawabinsa na maraba, shugaban karamar hukumar Malam Mannir Mu’azu ya yaba wa gwamnan kan ƙoƙarin da yake wajen harkar tsaro.

Ya nuna wa gwamnan takin zamani da ake sarrafa a yankin da alƙawarin tallafawa manoman rani guda 300.

By ukarofi