Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya gana da gwamnonin APC shida a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Litinin ne Shugaba Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da gwamnoni guda shida na jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Gwamnonin sun isa fadar ne da misalin ƙarfe 4 na yamma domin halartar zaman, wanda ya ɗauki tsawon ƙasa da sa’a guda ana yin sa.

Saidai babu wani ƙarin bayani akan musabbabin abinda aka tattauna a yayin haka duba da cewa ba a sanar da maƙasudin zaman ba.

Blueprint.ng ta ruwaito cewa waɗanda suka halarci zaman sune gwamnonin jihohin Jigawa, Umar Namadi; Edo, Monday Okpebholo; Ekiti, Biodun Oyebanji; Kogi, Usman Ododo; Sakkwato, Aliyu Sokoto; da kuma na Kebbi, wato Nasir Idris.

Haka kuma babu ɗaya daga cikin gwamnonin da ya yi tsokaci a kai bayan kammala zaman.

By Babaji