Sakkwato: Jami’an Sabon Birni sun musanta kashe-kashen masallaci yayin da sojoji suka daƙile hari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Birnin Jihar Sakkwato, Alhaji Ayuba Hashimu, ya ƙaryata rahoton cewa an kai farmaki a wani masallaci wanda aka yi zargin ya halaka limami da wasu masallata a yankin.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ce wani gidan jarida ne ya ruwaito cewa ƴan bindiga sun farmaki al’umma a wani masallaci da ke cikin garin Sabon Birni, inda suka halaka limami da wasu mamu tare da yin awon-gaba da wasu.

A wata hira da manema labarai, Shugaban ƙaramar hukumar ya musanta batun kai harin, inda ya ce kwatakwata hakan bai faru ba. “Labarin ƙarya ne”, inji Hashimu.

Haka ma Ɗan Majalisar Dokokin jihar da ke wakiltar Sabon Birni, Alhaji Aminu Boza a wata hira, wanda ya ƙaryata rahotannin da cewa babu wani masallaci da aka kai wa hari.

To saidai kuma wata majiya daga jami’an tsaro ta ce, dakarun sojoji sun yi arangama da ƴan bindiga a yankin Ƙauyen Gatawa da ke Sabon Birnin.

Ta bayyana cewa, da fari ƴan ta’addar sun fara fafatawa ne da wasu ƴan sa-kai a yankin kana daga bisani sojoji suka kai ɗauki tare da daƙile farmakin.

A cewar majiyar, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 da daren ranar Juma’a a hanyar Ɗan-Kamarawa da Gatawa.

By Babaji