Sanata Yar’adua ya ba al’ummar mazaɓarsa haƙuri

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A wata sanarwa da mataimakin sa na musamman kan yaɗa labarai ya fitar ya ce sanatan ya saurari kowa kuma yana tabbatar masu zai yi nazari da kuma kawo gyara.

Yar’adua ɗan Adam ne, duk ɗan Adam ajizine kuma ya san ƙauna tasa al’ummar sa basa son su ga wata matsala.

“Saboda haka ina bada haƙuri.A bamu lokaci kaɗan mu ƙara nazari domin fidda hanyoyi da za a yi gyara,”Inji Yar’adua.

Sanata Yar’adua ya yi godiya bisa shawarwari da masoyan ke badawa domin cigaba da wannan tafiya kuma domin tafiyar jam’iyyar su ta ƙara samun nasara.

“Ina so ku sani ina jin daɗin kishin da kuka nuna mani da ƙauna, bani da wani kamar ku,”Matawallen Katsina ya ce.

Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua shike wakilan Katsina ta tsakiya a jihar Katsina.

By ukarofi