
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa wasiƙar neman ta amince wa buƙatar tura dakarun tsaron Nijeriya zuwa Jamhuriyar Benin.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya karanta takardar yayin zaman majalisar na yau Talata.
Tinubu ya ce, matakin abu ne mai muhimmanci bisa la’akari da yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar kwanan nan.
Ya bayyana cewa, hakan tallafi ne ga ƙasar sakamakon neman agaji da Shugaba Patrice Talon ya yi jim-kaɗan bayan yunƙurin juyin mulkin ga shugaban Nijeriyar.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa, gwamnatin Benin tana fuskantar barazanar karɓe mulkinta na dimukraɗiyya da take tafiya a kai yanzu daga ɓangarorin da ke adawa da ita, wanda abu ne da ka iya haddasa fitina ga ƙasar da al’ummarta.
Don haka ne Nijeriya ta yanke shawarar tallafa mata ta hanyoyin da suka dace domin tseratar da tsarin mulkin ƙasar na yanzu da kuma bada kariya ga jagorori da al’ummarta.
