Lalacewar na’ura ce ta haifar da saukar jirgin sojojin Nijeriya a Burkina Faso ba shiri, inji NAF

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin aka shiga fargaba a shiyyar ƙasashen Sahel (AES) yayin da Mali, Nijar da Burkina Faso suka yi alla-wadai ta saukar gaggawa da jirgin C-130 na rundunar sojin Nijeriya ya yi a Burkina Faso, lamarin da ƙasar ta kira da saɓa wa dokokin sararin samaniyarta.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya auku ne a lokacin da jirgin ya yi jigilar dakarun Nijeriya 11 yayin da suak nufi ƙasar Portugal, inda babu shiri suka sauka a Bobo-Dioulasso, abinda hukumomin Nijeriya suka ce ya faru ne sakamakon gazawar na’ura ana tsaka da tafiya.

A wata sanrwa da gidan rediyon AES ya fitar, ya ce jirgin ya kutsa cikin sararin samaniyar Burkina Faso ne ba tare da samun izinin hukumomin ƙasar ba.

Duk da cewa ɓangaren Nijeriya ya yi ƙoƙarin kare dakarunsa ta dalilin tsaikon, hukumomin AES sun ce hakan abu ne da ka iya haddasa munanan al’amura.

Akan haka ne AES ta umarci rundunonin sojin sama da su kasance a faɗake na jiran umarnin buɗe wuta ga dukkan wani jirgi da ya saɓa wa dokokin sararin samaniyar yankinsu.

Saidai, a wata sanarwa da NAF ta fitar a yau Talata, ta ce ta samu labarin saukar gaggawa da jirgin jami’an nata ya yi, wanda a cewarta ya sauka cikin aminci kamar yadda yake a tsare-tsaren sufurin jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa.

A cewar Ehimen Ejodame, wato Daraktan hulɗa da jama’ar NAF, jirgin ya bar Legas ne a ranar Litinin domin zuwa Portugal, kana daga bisani tawagar kula da shi suka gano an samu matsalar na’ura da ka iya haddasa mummunan al’amarin, wanda hakan ya sa suka ɗauki matakin gaggawa na sauka a yankin.

By Babaji