Zargin badaƙala: EFCC ta rufe gidan Timipre Sylva na Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Julius Bokoru, wanda shi ne Mai taimaka wa tsohon Ƙaramin Ministan Albarkatun Fetur kuma tsohon gwamnan Bayelsa, Cif Timipre Sylva, akan harkokin yaɗa labarai, ya yi alla-wadai da rufe gidan maigidansa da ke Maitama a Abuja da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC ta yi a jiya Litinin.

Bokoru ya nuna rashin amincewa da matakin na EFCC wanda ya kira da “taka masa ƴancin mutunci” a matsayin na ɗaya daga cikin jagororin al’umma.

Tun a watan Nuwamba EFCC ta ayyana Sylva a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zargin sa da hannu a badaƙalar Dala miliyan 14.8, inda a lokacin ne jami’an leƙen asiri na sojoji suka kai samame gidan nasa na Abuja tare da kama ɗan uwansa da direbansa bisa zargin alaƙanta tsohon ministan da hannu a yunƙurin juyin mulki.

Saidai, Bokoru ya soki matakin EFCCn da cewa ba ta gayyaci Sylva ba gabanin kai samame gidansa duk da cewa tsohon ministan da kansa ya aike wa EFCC cewa ya amince ya amsa kiranta, lamarin da ya zama matsi a gare shi da iyalansa.

Akan haka ne Bokoru ya yi kira ga mai girma Shugaba Bola Tinubu da tsoma baki a al’amarin domin shawo kansa ta yadda za a kawo ƙarshensa cikin tsarin da dokar ƙasa ta amince da shi.

Ya kuma bayyana mai gidan nasa a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasa da suka yi mata hidima bisa kulawa da biyayya da kishi yayin riƙe da muƙaman da ya samu a gwamnati.

By Babaji