
Gwamnatin soji ta ƙasar Burkina Faso ta bayyana cewa ta tsare jami’an sojin Nijeriya guda 11 tare da ƙwace wani jirgin rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) bayan jirgin ya yi saukar gaggawa a cikin kasar.
Al’amarin ya faru ne bayan jirgin ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da samun izinin hukumomin ƙasar ba a jiya Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin, wanda ke ɗauke da kayan aiki, an tilasta masa yin saukar gaggawa bayan tasowarsa daga Nijeriya.
Haka kuma hukumomin Burkina Faso sun ce wannan karya dokar sararin samaniya ce, wadda ta tilasta su ɗaukar matakin tsaro akan waɗanda abin ya shafa.
A cewar sanarwar, jami’an tsaron ƙasar sun kwashe sojojin 11 zuwa inda ake gudanar da bincike, tare da tsare jirgin har sai an kammala dukkan matakan difulomasiyya da bincike akan al’amarin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, hukumomin Nijeriya ba su fitar da bayani ba a kai ba, saidai ana sa ran tattaunawar diflomasiyya za ta gudana domin warware al’amarin.
