
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar masu Shirya fina-finai ta ƙasa (MOPPAN) da haɗin-gwiwar Ƙungiyar ƴan fim ta ƙasa (AFMAN), sun nuna damuwa kan yadda ake ƙoƙarin mayar da su saniyar ware a harkokin Hukumar Kula da Fina-finai ta ƙasa NFC.
A wata wasiƙa zuwa ga Darakta Manaja na NFC reshen Jihar Filato, da Shugaban MOPPAN da AFMAN (Shehu Hassan Kano da Salisu Mohammed Officer) suka fitar, ƙungiyoyin sun bayyana damuwarsu bisa yadda ake nuna musu wariya da sakaci da al’amuransu waɗanda ke cigaba da yawaita daga ɓangaren wakilan NFC na Arewa.
Sun ce, gabanin daraktan ya kama aiki, hukumar tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta kiyaye aiki tare da ƙungiyoyin ta yadda take bada gudumuwa ga ci-gaban fina-finansu, ayyukan al’adu, inganta matasa da haɗin kan ƙasa ta harkar fim.
Haka kuma, sun bada misali da taron Zuma festival da NFC ta shirya na kwanan nan, wanda duk da cewa MOPPAN da AFMAN suna da muhimmanci da babban rawa da za suke da shi a kai, babu wata gayyata ta musamman da aka aika musu.
Sannan, sun bayyana cewa ci-gaban ƙasa ta ayyukan fasaha musamman ta masana’antun fina-finai zai samu ne yayin da aka samu haɗin-gwiwa tsakanin dukkan ɓangarorin ƙasa da damawa da su ta yadda kowane ɓangare zai bada tasa gudunmawar.
Don haka suka yi kira ga ɓangaren da abin ya shafa da ya yi nazari akan al’amarin tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen warware matsalolin duba da yadda Kannywood, wadda ita ce masana’antar fim da ke kan gaba a arewacin Nijeriya ke bada gagarumar gudumawa a fannin.
