Uwargidan Gwamnan Zamfara ta taya Remi Tinubu murna bisa naɗa ta sarautar Yeye Asiwaju Ile Oodua

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Huriyya Dauda Lawal, ta taya uwargidan shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, murnar naɗa ta a matsayin Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua a Ile-Ife da ke Jihar Osun.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakatariyar yaɗa labarai na Uwargidan Gwamnan Jihar ta Zamfara, Rabi Yusuf kuma ta miƙa wa Blueprint.

Naɗin na daga cikin ayyukan da aka yi na cika shekaru 10 na sarautar Ooni na Ife, Mai Martaba Sarkin Ife, Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II, wanda ya samu halartar sarakunan gargajiya, manyan jami’an gwamnati, da sauran manyan baƙi daga sassan ƙasar nan.

Hajiya Huriyya ta bayyana irin karramawar da aka yiwa Sanata Oluremi a matsayin abunda ya dace.

Ta yi nuni da cewa, hakan na nuni da irin jajircewar da ta yi na ci gaban kasa, da tallafa wa mata da kuma bayar da gudunmawar ƙarfafa iyalai da al’ummomi ta hanyar wasu tsare-tsare na jin ƙai da manufofi.

Ta ƙara yaba wa Ooni na Ife saboda zaɓar Sanata Oluremi Tinubu don bata wannan muƙamin don girmama wa.

A cewarta, shawarar da Basaraken ya yanke na bai wa Uwargidan Shugaban Ƙasa sarautar ya nuna cewa ta fahimci shugabancinta, tasirinta da kuma hidimar da ta daɗe tana yi wa ƙasa.

Hajiya Huriyya ta jajjada cewa naɗin Sanata Oluremi Tinubu ya nuna muhimmiyar rawar da Masarautun gargajiya ke takawa wajen amincewa da ayyukan gwamnati masu ma’ana.

Hajiya Huriyya Dauda ta kuma yaba da ƙoƙarin Ooni na kiyaye al’adun Najeriya da kuma haɓaka haɗin kai ta hanyar shugabanci a gargajiyance a Masarautar sa.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa bikin ya nuna zunzurutun al’adun Yarabawa da nuna muhimmancin masarautun gargajiya wajen haɓaka haɗin kai da alfahari dabasali da kuma cigaban ƙasa.

By ukarofi